Is this your podcast?
Sign up to track ranks and reviews from Spotify, Apple Podcasts and more
Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle
Shirin al´adu, addinai da kuma zamantakewa tsakanin al´ummomi dabam-dabam a duniya. Taba Ka Lashe shiri ne da ke duba batutuwan da suka shafi al'adu da zamantakewa tsakanin al'ummomi da mabiya addinai dabam-dabam a duniya da zummar kyautata zamantakewarsu, zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakani. Muna gabatar muku da shirin ta rediyo a kowane mako, kuna kuma iya sauraronsa a shafinmu na Internet da kuma ta kafar Podcast.
Listen now
Recent Episodes
Shirin ya duba rayuwar 'yan Nijar mazauna birnin Hamburg a tarayyar Jamus. Wasu daga cikin 'yan Nijar din sunn shafe kusan shekaru 18 zuwa 30 a kasar Jamus tare da iyalensu.
Published 01/08/20
Shirin ya dubi irin yadda kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Nijar da Senegal suka rabauta da masallatai da makarantu da wasu kasashen musulmi irin su Saudiyya da Turkiyya da Iran suka samar. Wasu na ganin hakan wata hanya ce ta cusa wasu akidu. A saurari shirin don jin karin batutuwa.
Published 12/31/19
Shirin na wannan karo ya duba batun tsarin tafiyar da ilimi a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu a Jamus da kuma irin bambancin da ke da akwai a tsakaninsu da kuma wanda ke da akwai tsakanin Jamus da Afirka.
Published 12/24/19
Do you host a podcast?
Track your ranks and reviews from Spotify, Apple Podcasts and more.
See hourly chart positions and more than 30 days of history.
Get Chartable Analytics »