Lafiya Jari ce - Najeriya ta samar da sabon salon wayar da kan al’umma game da annobar Corona
Listen now
Description
Shirin wannan mako zai yada zango ne a tarayyar Najeriya inda gwamnatin kasar ta kara fidda sabon salon wayar da kan al’umma game da tabbatuwar annobar Corona, da kuma rungumar allurar rigakafin ta. Wannan ce ta sa gwamnatin ta yi hadin gwiwa da wasu da kungiyoyin mata don taka irin tasu rawar game da fatattakar cutar a kasar a wani taro da hukumar lafiya matakin farko ta shirya d kungiyar mata mai taken MUM. Rukayya Abba Kabara ce ta jagoranci shirin a yau.