DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019)
Listen now
Description
DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019) [1][2] Cikin shirin za a ji yadda wasu al'umomi ke bayyana muhimmancin kafar sadarwar rediyo a rayuwarsu ta yau da kullum, dai lokacin da ake ranar rediyo ta duniya. A Najeriya kuwa mazauna yankunan karkara ne ke damuwa da yawan alkawura da 'yan siyasa ke dauka ba tare da cikawa ba. Host: Munta Gayuwa* Nigeria: Za mu ji yadda mazauna yankunan karkara a Najeria suke cewa suna cikin halin taƙaici na roman baka da 'yan siyasar ƙasar ke yi musu, tsawon shekaru da ƙasar ta kama mulki irin na demokraɗiya. Toh wane irin alƙauran ne wadannan 'yan siyasa ke yi wa wadannan mutane na karkara?"In mun ci zaɓe, za mu yi muku hanya. In mun ci zaɓe, za mu kawo muku wuta, asibiti, da sauran abubuwa. Amma ko ɗaya, ba wanda ya taɓa cika mana. Wani pole-waya an kafa a nan ya kai har shekara goma sha biyu (12), amma wallahi ba a zo yin komai ba!" Nigeria: Muna tafe da rahoto kan wannan matsala. Hakannan kuma za'a ji al'ummar Fulani da dokar hana kiwo ta shafa a jihar Benue da ke tsakiyar Najeriyar. Sun buƙaci kariya ne daga jami'an tsaro a duk inda suke don basu damar zaɓe kamar sauran 'yan ƙasar Najeriyar. World Radio Day 2019: Yayin kuma da ake ranar rediyo ta duniya, za mu ji yadda wasu al'ummomi ke bayyana mahimmancin kafarta sadarwa a garesu. Morocco: Hukumomi a ƙasar Morocco, sun kama wasu Faransawa da suka ce suna ɗaukar nauyin ƙungiyar nan ta IS. Nigeria: Mutane da dama sun mutu lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe na shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya. Thailand: Wasu fursunoni, wato 'yan ƙabilar Uyghir, sun tsere daga hannun jami'an tsaro a ƙasar Thailand.
More Episodes
Daga Laraba 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao Ga shirin mu na podcast wanda Halima Djimrao ce ta jagoranta tare da sauran abokan aiki. Shiri ne akan yadda ƴan ƙabilar Igbo Musulmi ke cikin tsangwama da barazana a yankin su na kudu maso gabashin Najeriya, saboda haka...
Published 05/24/21
Published 05/24/21
Allah akbar! Wannan muryar marigayi, Malam Habibu Sani Babura kenan, yayin da yake lacca a wajen taron daliban Hausa  a Jami'ar Bayero ta Kano. Yau shekara biyu da rasuwar Malam (3/8/2018. Allah ya jikansa da rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya Sada shi da Annabi, Allah ya bashi aljanna...
Published 09/04/20