Episodes
Daga Laraba 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao
Ga shirin mu na podcast wanda Halima Djimrao ce ta jagoranta tare da sauran abokan aiki. Shiri ne akan yadda ƴan ƙabilar Igbo Musulmi ke cikin tsangwama da barazana a yankin su na kudu maso gabashin Najeriya, saboda haka da yawan su, sun gwammace su yi hijira zuwa arewa.
Podcast Trailer: https://youtu.be/qzLb2V9521U
Published 05/24/21
Allah akbar! Wannan muryar marigayi, Malam Habibu Sani Babura kenan, yayin da yake lacca a wajen taron daliban Hausa a Jami'ar Bayero ta Kano.
Yau shekara biyu da rasuwar Malam (3/8/2018. Allah ya jikansa da rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya Sada shi da Annabi, Allah ya bashi aljanna Firdausi).
Published 09/04/20
Shirin Arewa Radio kan #RanarHausa2020 tare da Faisal Abdullahi (@BANNigeria) da Mazhun (@HausaTranslator) na Bloggers Association of Northern Nigeria.
Published 08/25/20
Shirin Daga Taskar Hausa inda aka tattauna da Farfesa Aliyu Muhd Bunza da Dakta Abdulƙadir L Koguna da kuma Dakta Muhammad Suleiman A., a kan Ranar Hausa ta Duniya wato 26 ga watan Ogusta 2020.
Ku kasance da shirin a yau, Lahadi, ƙarfe 8 zuwa 9 na dare. Daga Guarantee Radio 94.7 Kano a ranar Lahadi Aug 23, 2020.
Za ku iya saurara kai tsaye daga ko'ina a www.guaranteeradio.com
Published 08/24/20
Kai tsaye acikin shirin #ZararBubu da @CDDWestAfrica ke daukar nauyin kawowa masu sauraro dan wayar da kai game da #LabaranBogi, Dr. Nura Ibrahim ke jawabi game da yadda za'a kaucewa labaran bogi a shafukan sada zumunta na zamani.
Related links:
https://twitter.com/CDDWestAfrica_H/status/1286959730716545026
https://youtu.be/aOgO9amMnl4
#ADainaYadaLabaranKarya #ADenaYadaLabaranKarya #StopFakeNews #StopSpreadingFakeNews #FakeNews #HausaFakeNews #FakeHausaNews #LabaranBogi
Published 07/25/20
Jamila Kabiru Fagge da Bashir Ahmad sun tattauna akan #RanarHausa August 26, 2015
Published 07/25/20
DW Hausa - Taba ka Lashe - Tasirin Wasan Kwaikwayo 2020.05.28
Mai gabatarwa: Fauziyya Dauda
Published 05/28/20
Full transcript: http://hausadictionary.com/hausaradio/20200508
1 Kanun Labaran DW Hausa - Shirin Yamma 08.05.2020
2 Kanun Labaran VOA Hausa - Shirin Dare 2030 UTC (30:00) - Mayu 08, 2020
3 Kanun Labaran RFI Hausa 20h00 - 20h17 GMT - Labarai 08/05 20h00 GMT
4 Kanun Labaran Talabijin na BBC Hausa 08/05/2020
5 Kanun Labaran Radio VOH 3 - 20200508
Published 05/09/20
Show notes and transcript > Cikakken bayanin wannan podcast din: http://bit.ly/BBCHausaSafe20190522
Send in a voice message:
https://anchor.fm/hausaradio/message
Published 05/22/19
Host (mai gabatarwa): Abdullahi Isa
K'asashe masu k'arfin tattalin arziki da aka sani da G7 sun gudanar da taro a birnin Paris, taro da ya mayar da hankali zuwa ga batutuwan da suka shafi kiwon lafiya.
Yayin da gwamnatin k'asar Venezuela da kuma 'yan adawa da ke cigaba da kai ruwa rana suka soma tattaunawa a Norway.
Za ku ji cewa shafin sada zumunta na Facebook ya san da rusar wasu shafuka 216 na k'arya wadanda ake amfani da su domin rubuta kalamai ko kuma batutuwa da ba su dace ba zuwa...
Published 05/18/19
Hosts (masu gabatarwa): Grace Alheri Abdu, Baba Yakubu Maƙeri
US: Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya sanar da wani sabon tsarin dokan bakin haure, wanda zai [unintelligible] gurbin baki d’ayan dokan bakin haure a nan Amurka.
US: A wata sabuwa kuma Donald Trump ya ce yana k'ir da zaton Amurka ba za ta shiga da yak'i a Iran ba a lokacin da ake k'ara samun tankiya a gabas ta tsakiya.
Burkina Faso: Bayan haka, ministan harkokin wajen Burkina Faso ya yi kira ga k'asashen duniya...
Published 05/18/19
Host Mai gabatarwa: Aisha Sharif Baffa
Yau ce dai ranar yak'i da cutar hawan jini, wato hypertension, ta duniya. Toh ko ya mutum zai kare kansa daga kamuwa da wannan cuta?
"Farko, mutum ya zama cewa yana yawan motsa jiki. Sannan kuma a … Read More at http://bit.ly/BBCHausaSafe20190517
Thank you for subscribing. Share this episode.
Send in a voice message:
https://anchor.fm/hausaradio/message
Published 05/17/19
DW Hausa Shirin Safe 01.03.2019 [1]
Masana tattalin arziki da hada-hadar kudi a Najeriya, sun bada shawarar cewa ya kamata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta bada himma wajen raya tattalin arzikin kasar musamman a yankin arewacinta domin magance matsalolin da ke addabar yankin.
Hosts: Muntaqa Ahiwa
Nigeria: Cikin shirin za'a ji yadda masana suka soma baiwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shawara kan buƙatar zaburar da harkokin tattalin arziƙi, musamman ma na arewacin ƙasar da ke...
Published 03/01/19
ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
Hosts: Abdullahi Salihu*
Nigeria Elections 2019: Wasu daga cikin jami'an gwamnatin APC a Najeriya sun nuna ɓacin ransu matuƙa dangane da yadda ƙungiyoyi na dattijan arewa da ma wasu daga ɓangaren kudancin ƙasar suka nuna goyan bayansu ga ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyar adawa ta PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar.
Ethiopia: Za mu duba yadda masana suke kallon kawo ƙarshen taron shugabannin ƙasashen Afrika, wanda aka gudanar a birnin Adis...
Published 02/14/19
BBC Hausa Shirin Rana (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
Hosts: Sulaiman Ibrahim Katsina
Nigeria Elections 2019:
A yau ne a Najeriya aka shirya soma rarraba kayan aiki don zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe ranar Asabar.
Suma masu sa ido, sun buɗe sansaninsu a yau.
Wani kuma, wanda da alama ya fi kowa niyar zaɓen, tun jiya ya isa rumfar zaɓen. Inda yake shirin yin kwanaki uku yana jira kafin a soma kaɗa ƙuri'a."Tun jiya, ƙarfe goma sha ɗaya da rabi (11:30) na bar gida na. Na...
Published 02/14/19
BBC Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
Liberia: In gano gawar mutane biyar amma a mahaƙar ma'adinai ta gwal wadda ta rifta a arewacin Liberia a makon da ya wuce.
USA, Yemen: 'Yan majalisar Amurka sun gabatar da uzurin da zai janyowa dakarun ƙasar su janye daga Yemen.
Nigeria Elections 2019: Yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da zaɓe a Najeriya, masu larura ta musamman na ƙorafi kan jami'an tsaro a rumfunan zaɓe."Dubu biyu da sha biyar...
Published 02/14/19
BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
Nigeria: A Najeriya, an kai wa waɗansu tagwayen hare-hare kan ayarin gwamnan jihar Borno a lokacin yaƙin neman zaɓe a garin Gamboru.
Nigeria Elections 2019: Jam'iyar PDP ta zargi gwamnatin APC da yi mata kwitingila na hana ta yin filin yin taro a Abuja: "Gashi bayan mun yi gangamin mutane, daga ko'ina sun taho, har da masu hawan jakuna da dawakai. Da muka je, muka tarar an sa kwaɗo, an hana." Sai dai kuma,...
Published 02/14/19
VOA Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba.
Nigeria: Ministan tsaron Najeriya, Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya ƙaryata jita-jita da ake yi na cewa jami'an ƙasar basu da kayan aiki."Ko ƙasar America, ko ƙasar Ingila (England), ko ƙasar Russia, ba za su ce suna da isasshun kaya da suka ishe su ba.
Muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, wato EFCC, Ibrahim Mago, ya ce za su gurfanar da masu...
Published 02/14/19
VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba.
USA, Iran: Amurka tana tuhumar wata tsohuwar jami'ar sojan samanta wadda ta canja sheƙa zuwa ɓangaren Iran da yin mata leƙan asiri.
USA: Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu bai tsaida shawarar rattaba hannu ko a'a kan ƙudurin bai ɗaya da jam'iyyu suka cimma ba wanda ya tanadi kuɗin gina katanga.
USA: Majalisar wakilan Amurka mai rinjayin 'yan Democrats, ta kaɗa kuri'ar...
Published 02/14/19
RFI Hausa's coverage of World Radio Day (0:00-1:16)
DW Hausa's coverage (1:16-4:54)
BBC Hausa's coverage (4:54-8:49)
Published 02/13/19
DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019) [1][2]
Cikin shirin za a ji yadda wasu al'umomi ke bayyana muhimmancin kafar sadarwar rediyo a rayuwarsu ta yau da kullum, dai lokacin da ake ranar rediyo ta duniya. A Najeriya kuwa mazauna yankunan karkara ne ke damuwa da yawan alkawura da 'yan siyasa ke dauka ba tare da cikawa ba.
Host: Munta Gayuwa*
Nigeria: Za mu ji yadda mazauna yankunan karkara a Najeria suke cewa suna cikin halin taƙaici na roman baka da 'yan siyasar ƙasar ke yi musu, tsawon...
Published 02/13/19
BBC Hausa Shirin Hantsi (Wed Feb 13th 2019) [1] [2]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
South Korea: Hukumomin Koriya ta Kudu, sun musunta iƙirarin shugaba Trump kan ƙara yawan kuɗaɗen da take baiwa sojin Amurka a ƙasar ta.
Sudan: Jami'an tsaro sun cafke wasu daga cikin farfesoshin jami'o'i a birnin Khartoum.
Nigeria: Kwanaki uku kafin a yi zaɓen shugaban ƙasa, matasa da suka fito takaran muƙamai sun ce salon mulkin su zai banbanta da na 'yan baya."Almazaranci da kuɗin mutane, da rashin...
Published 02/13/19
BBC Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019 - 6:30am NGT) [1][2]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
Venezuela: Shugaban 'Yan adawa a Venezuela, ya sha alwashin shigar da kayan agaji. Duk kuwa da cewa shugaba Maduro ya ƙi amincewa da hakan.
Nigeria: Ana cigaba da cece-kuce kan shugaba Muhammadu Buhari a jihar Zamfara. Da ake cewa hakan zai iya haddasa fitina. Toh sai dai kuma magoya bayanshi sun ce an yi masa mummunar fahimta.
Shin kuma ko wace rawa ce rediyo ke takawa a rayuwar al'umma? Muna...
Published 02/13/19
BBC Hausa Shirin Yamma (Tue Feb 12th 2019 - 8:30pm NGT) [1][2]
Hosts: Aminu Abdulkadir
Sudan: Jami'an tsaron ƙasar Sudan sun tsare wani rukunnin shegunnan malamai na jami'o'i. Da suka yi zanga-zangar ƙin jinin shugaba Umar Al-Bashir a Khartoom - babban birnin ƙasar.
Nigeria: Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wasu mutane dangane da gobarar da tashi a wani ofishin hukumar zaɓe, yau a jihar Anambara. Gobarar ta haddasa ɓarna."Toh, har yanzu dai ba mu kai ga tantance yawan adadin wannan...
Published 02/13/19