Description
ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
Hosts: Abdullahi Salihu*
Nigeria Elections 2019: Wasu daga cikin jami'an gwamnatin APC a Najeriya sun nuna ɓacin ransu matuƙa dangane da yadda ƙungiyoyi na dattijan arewa da ma wasu daga ɓangaren kudancin ƙasar suka nuna goyan bayansu ga ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyar adawa ta PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar.
Ethiopia: Za mu duba yadda masana suke kallon kawo ƙarshen taron shugabannin ƙasashen Afrika, wanda aka gudanar a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha, da kuma abubuwan da taron ya cimmawa game da yiyuwar aiwatar da su a aikace.
France: Za mu duba batun matakan da sojojin gwamnatin ƙasar France suka ɗauka na kare wanda ya juya mulki da suka ce an yi yunƙurin aiwatarwa a ƙasar Cadi.
Iran, Lebanon: Za a ji sharhin [ unintelligible: bayan labaran? ] wadanda suka yi magana akan ziyarar wadansu harkokin wajen Iran a ƙasar Lebanon.
Shirin Ko Kun San, Kaza a kan dame, shirin labaran wasannin mako.
Venezuela: Shugaban ƙasar Venezuela ya ce ƙasar za ta zamai wa Amurka Vietnam matuƙar ta kai mata hari.
Bahrain: An cika shekaru takwas da fara yunƙurin al'umma a ƙasar Bahrain.
China: ƙungiyar kare hakkin bil Adama (human rights) na ƙasashen duniya sun zargi ƙasar China da take hakkokin musulmi.
Daga Laraba 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao
Ga shirin mu na podcast wanda Halima Djimrao ce ta jagoranta tare da sauran abokan aiki. Shiri ne akan yadda ƴan ƙabilar Igbo Musulmi ke cikin tsangwama da barazana a yankin su na kudu maso gabashin Najeriya, saboda haka...
Published 05/24/21
Allah akbar! Wannan muryar marigayi, Malam Habibu Sani Babura kenan, yayin da yake lacca a wajen taron daliban Hausa a Jami'ar Bayero ta Kano.
Yau shekara biyu da rasuwar Malam (3/8/2018. Allah ya jikansa da rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya Sada shi da Annabi, Allah ya bashi aljanna...
Published 09/04/20