Description
BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
Nigeria: A Najeriya, an kai wa waɗansu tagwayen hare-hare kan ayarin gwamnan jihar Borno a lokacin yaƙin neman zaɓe a garin Gamboru.
Nigeria Elections 2019: Jam'iyar PDP ta zargi gwamnatin APC da yi mata kwitingila na hana ta yin filin yin taro a Abuja: "Gashi bayan mun yi gangamin mutane, daga ko'ina sun taho, har da masu hawan jakuna da dawakai. Da muka je, muka tarar an sa kwaɗo, an hana." Sai dai kuma, ana ta ɓangaren, APC ta musanta wannan zargin: "Na farko dai, fili na gwamnati ne kuma na tabbata akwai ƙa'idoji wadda ake bi. Maganar cewa wai yau an hana su taro domin wani abu... tsoron faɗuwa ne, shi ya sa suke neman duk ta hanyar da za'a bi a tayar da hankali."
Sudan: BBC ta bankaɗo wani wuri da ake tsare masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati tare da azabtar da su a ƙasar Sudan.
Taƙaitaccen labarin wasanni.
Daga Laraba 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao
Ga shirin mu na podcast wanda Halima Djimrao ce ta jagoranta tare da sauran abokan aiki. Shiri ne akan yadda ƴan ƙabilar Igbo Musulmi ke cikin tsangwama da barazana a yankin su na kudu maso gabashin Najeriya, saboda haka...
Published 05/24/21
Allah akbar! Wannan muryar marigayi, Malam Habibu Sani Babura kenan, yayin da yake lacca a wajen taron daliban Hausa a Jami'ar Bayero ta Kano.
Yau shekara biyu da rasuwar Malam (3/8/2018. Allah ya jikansa da rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya Sada shi da Annabi, Allah ya bashi aljanna...
Published 09/04/20