Description
BBC Hausa Shirin Hantsi (Wed Feb 13th 2019) [1] [2]
Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
South Korea: Hukumomin Koriya ta Kudu, sun musunta iƙirarin shugaba Trump kan ƙara yawan kuɗaɗen da take baiwa sojin Amurka a ƙasar ta.
Sudan: Jami'an tsaro sun cafke wasu daga cikin farfesoshin jami'o'i a birnin Khartoum.
Nigeria: Kwanaki uku kafin a yi zaɓen shugaban ƙasa, matasa da suka fito takaran muƙamai sun ce salon mulkin su zai banbanta da na 'yan baya."Almazaranci da kuɗin mutane, da rashin tsaro da ya addabi mutane, da yaudara, da sauransu... da aka saba ganin 'yan siyasa suna yi. Wanda mu ba mu fito ba da wannan..."
Cameroon: Za kuma ku ji kiraye-kirayen da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ke yi wa hukumomin Kamaru domin su sako wata ɗaliba da ake tsare ita.
Daga Laraba 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao
Ga shirin mu na podcast wanda Halima Djimrao ce ta jagoranta tare da sauran abokan aiki. Shiri ne akan yadda ƴan ƙabilar Igbo Musulmi ke cikin tsangwama da barazana a yankin su na kudu maso gabashin Najeriya, saboda haka...
Published 05/24/21
Allah akbar! Wannan muryar marigayi, Malam Habibu Sani Babura kenan, yayin da yake lacca a wajen taron daliban Hausa a Jami'ar Bayero ta Kano.
Yau shekara biyu da rasuwar Malam (3/8/2018. Allah ya jikansa da rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya Sada shi da Annabi, Allah ya bashi aljanna...
Published 09/04/20