Kasuwanci - Faduwar darajar Naira na ci gaba da haifar da tsadar rayuwa a Najeriya
Listen now
Description
Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba kasuwar musayar kudin kasa da kasa a Najeriya inda kudin kasar na Naira ke cigaba da faduwa, yayin da kudaden kasashe ketare musamman Dallar Amurka, ke tashin goron-zabi. Menene tasirin wannan hawa-hawan farashin na Dalla ga tattalin arzikin Najeriya kuma ina mafita? wadandan sune abin da shirin ya yi nazari akai.