Episodes
Published 09/25/24
Shirin 'Kasuwa a Kai Miki Dole' tare da Garba Aliyu Zaria ya yi tattaki zuwa babbar kasuwar kayan gwari ta Mile 12 da ke birnin Legas inda ya zanta da shugabannin kasuwar da sauran masu ruwa da tsaki kan halin da take ciki, bayan kawo karshen rigingimu a tsakanin kabilun da ke cudanya da juna.
Published 12/29/21
Shirin Kasuwa a kai miki dole tare da Ahmed Abba ya yada zango jihar Plateau da ke arewacin Najeriya, inda gwamnatin jihar, ta amince da rage kudin yin takardun mallakar gidaje da filaye da kashi 50, don bai wa jama’a damar samunsu cikin sauki.
Published 12/08/21
Shirin kasuwa a kai miki dole tare da Ahmed Abba ya yi dubi kan matakin kamfanin man Najeriya na cire tallafin mai, wanda zai sauya farashin zuwa kusan ninkin yadda ake saya a yanzu. Tuni dai wannan batu ya haddasa cecekuce a sassan kasar wadda al'ummarta ke fama da matsin rayuwa.
Published 12/01/21
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi duba kan yadda 'yan Najeriyar ke fuskantar matsalar muhalli, duk da kokarin da gwamnati ke yi na samar da gidaje amma kadai ga daidaikun ma'aikatan gwamnati na yawansu bai taka kara ya karya ba. Ayi saurare Lafiya.
Published 11/24/21
Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi duba kan yadda hukumomin Jamus suka dakatar da aikin ginin bututun iskar gas da kamfanin kasar Rasha ke jagoranta sakamakon takaddamar da ta biyo bayan rashin bin dokoki daga kamfanin. Ayi saurare lafiya.
Published 11/17/21
Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yada zango ne jihar Adama dake arewacin Najeriya, inda yayi nazari kan halin da al’umma ke ciki na karancin man fetur.
Published 11/10/21
Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba taron kasa da kasa kan Sauyin Yanayi a birnin Glasgow na kasar Scotland, da anniyar kasashen duniya na rage amfani da duk wani  makamashi dangin Manpetur da masana ke cewa na taimakawa wajen dumamar yanayi da gurbata muhalli, inda shirin yayi nazarin kan tasirin wannan lamari ga tattalin arziki.
Published 11/03/21
Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan makon tare da Ibrahim Malam Goje ya duba sabon kudin yanar gizo na eNaira da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar, domin dacewa da zamani wajen farfado da tattalin arziki Najeriya da kuma saukaka hada-hadar kudade a yanar gizo.
Published 10/27/21
Shirin 'Kasuwa a kai miki Dole' na wannan mako ya maida hankali ne kan wani gagarumin taro da kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya MAN ta shirya a birnin Lagos dake Kudancin kasar, yayin da take bukin cikar ta shekaru 50 da kafuwa.
Published 10/20/21
Shirin Kasuwa A Kai Miki Jari na wannan mako ya yi nazari ne kan kalaman shugaban Najeriya Muhammdu Buhari, inda ya ce, tattalin arzikin kasar na habbakar da ba a taba ganin irinta ba tun bayan darewarsa kan karagar mulki. Sai dai tuni 'yan Najeriya suka bayyana shakku kan wadannan kalaman lura da yadda rayuwar ta yi tsada domin kuwa kusan kowacce rana farashin kayayyakin masarufi musamman abinci na tashin goron-zabi.
Published 10/13/21
Shirin na wannan makon ya maida hankali ne kan tallafin zangon karshe na gwamnatin Najeriya na rage radadin annobar korona, sannan kuma ya yi dubi kan wani shirin tallafa wa mata da hukumar SMEDAN ta yi a birnin Legas cibiyar kasuwancin kasar.
Published 10/06/21
Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba, ya yada zango a jihar Agadas da ke arewacin jamhuriya Nijar, yankin da matsalar tsadar rayuwa ke cigaba da tayar da hankullan magidanta.
Published 09/29/21
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan yunkurin Najeriya na sake neman bashin kudi har na dala biliyan 4 da Euro miliyan 710 daga kasashen waje domin cike gibin kasasfin kudin wannan shekara ta 2021, lamarin da ya jawo kace-nace a fadin kasar. Ayi saurare Lafiya
Published 09/22/21
Shirin Kasuwa a kai miki dole tare da Ahmed Abba wanda ya yi duba kan dambarwar da ta kunno kai tsakanin jihohin Lagos da Rivers da kuma gwamnatin Tarayyar Najeriya, bayan da jihohin suka bukaci basu damar cin gajiyar kudaden harajin VAT maimakon aikasu asusun ajiyar Tarayya.
Published 09/15/21
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba ya yi duba kan halin da 'yan kasuwar jihar Sokoto ke ciki bayan gobarar babbar kasuwar jihar ta farkon shekarar nan.
Published 09/08/21