Episodes
Yau Shirin 'Kasuwa A Kai Miki Dole' zai ya yada zango ne jamhuriyar Nijar, inda leka wani yanki da aka fara hako zinare, wato kauyen Kwandago dake cikin gundumar Madarounfa da ke jihar Maradi. wanda yanzu haka ‘yan kasashen Afirka ke tururuwar domin gudanar da wannan sabga ta arziki.
Published 09/01/21
Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya tattauna da masana kan matakin babban bankin Najeriya CBN na dakatar da baiwa kamfanonin 'yan canji kudaden kasashen waje.
Published 08/25/21
Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi nazari kan sabuwar dokar man fetur da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu. 
Published 08/18/21
A cikin shirin kasuwa. a kai miki dole,Bashir Ibrahim idris ya duba halin da ake ciki a Najeriya musaman bayan da wani bincike ya nuna cewa matsalar tsaro ta sa yan kasuwa kaura daga yankunan su zuwa kasashen waje. A cikin shirin za ku ta yada binciken ya nuna cewa jihar Gombe ce sahun gaba inda da dama daga cikin yan kasuwa a jihar suka kaura.
Published 08/11/21
Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan mako ya maida hankali ne dangane da shirin gwamnatin Najeriya na tallafawa manoma da kuma kananan sana’o’i. Shirin wanda Babban Bankin Najeriya CBN ya kirkirir karamin bankin tsimi da tanadi na musamman da akayi wa suna da NIRSAL dake tallafawa manoma da kananan ‘yan kasuwa basuka maras kudin ruwa cikin sauki, batare da jingina ba, kamar yadda aka saba a wasu bankunan kasuwanci.
Published 07/14/21
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba, a yau ya mayar da hankali kan tsadar rayuwa da kuma tashin farashin kayaki a kusan ilahirin sassan Duniya, ko da ya ke lamarin ya tsananta a Najeriya kasar da alkaluma ke nuna yadda ake samun karuwar matalauta a kowacce rana. 
Published 07/07/21
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole'  ya tattaunawa ne dangane da matsaloli ko asarar da matakin kasar Saudiya da hana aikin hajjin bana ya janyo, inda shirin ya yada zango jamhuriyar Nijar.
Published 06/30/21
Shirin Kasuwa akai miki dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan matakin kasar Saudiya na hana mahajjata aiwatar da aikin hajjin bana, matakin da ya haddasawa kamfanoni da dama asarar miliyoyin kudade. Ayi saurare Lafiya.
Published 06/24/21
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya maida hankali ne, dagane yadda takura da fulani makiyaya ke fuskanta a kudancin Najeriya ke shafar harkokin kiwo da safarar dabbobi daga arewaci zuwa kudancin kasar.
Published 06/16/21
Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi nazari kan muhimman kanana da matsakaitan masana'antu ga tattalin arzikin Najeriya, dai dai lokacin da karancin lantarki ke taka muhimmiyar rawa wajen durkushewarsu. A yi saurare lafiya.
Published 06/09/21
Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan makon yayi nazari ne kan halin da 'yan kasuwa suka shiga na cigaba da akasinsa sakamakon tasirin rufe iyakokin da Najeriya tayi tsakaninta da makwaftanta.
Published 06/03/21
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya duba batun musabbabin tsadar Siminti da kuma karuwar bukatarsa a Tarayyar Najeriya duk kuwa da matsin tattalin arziki da ake fama da shi, saboda matsalolin tsaro da annobar korona.
Published 05/26/21
Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba kasuwar musayar kudin kasa da kasa a Najeriya inda kudin kasar na Naira ke cigaba da faduwa, yayin da kudaden kasashe ketare musamman Dallar Amurka, ke tashin goron-zabi. Menene tasirin wannan hawa-hawan farashin na Dalla ga tattalin arzikin Najeriya kuma ina mafita? wadandan sune abin da shirin ya yi nazari akai.
Published 05/19/21
A cikin shirin 'Kasuwa A Kai Miki Dole', Ahmed Abba ya duba yadda dimbim 'yan Najeriya ke kwarara zuwa Jmhuriyar Nijar don gudanar da kasuwanci sakamakon matsin tattalin arziki.
Published 05/12/21
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' tare da Ahmed Abba ya yada zango ne jihar Barno dake Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ya yi nazari kan halin da al’umma suka shiga masamman a wannan lokaci na watan Ramadana, sakamkon rashin wutan lantarki da suka kwashe sama da watanni uku suke ciki, bayan da Boko Haram ta lalata turakun da ke kai wutan lantarki jihar.
Published 05/05/21
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida hankali ne dangane da ziyarar da karamin Ministan Faransa mai kula Kasuwancin Kasashen Waje, Franck Riester, ya kawo  Najeriya da zummar karfafa alakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu da kuma mika goran gayyata ga mahalarta manyan taruka biyu na tattalin arzikin Afrika- Faransa da shugaba Emmanuel Macron zai dauki nauyi a watan Mayu da kuma Yuli mai zuwa.
Published 04/28/21
Shirin Kasuwa akai miki Dole tare da Ahmed Abba ya yi Nazari ne kan halin da ake ciki dangane da Shirin gwamnatin Najeriya na kwarmato bayanan sirri kan cin hanci da rashawa ko kuma Whistle blowing a turance, wada ta yi alkawarin bada lada akai, to sai dai wasu na korafin cewa sun bada bayanan sirri ba tare da basu sisin kobo ba, hasalima an jefa rayuwarsu cikin hadari.
Published 04/28/21
Shirin Kasuwa a kai miki Dole tare da Ahmed Abba ya leka sabuwar kasuwar Akinyele a jihar Oyo, kasuwar da wasu hausawa suka koma bayan hatsaniyar da aka samu a kasuwar SASA da ya yi sanadiyyar rasa dimbin rayuka da dukiyoyin jama'a.
Published 04/07/21
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba, ya leka ne janhuriyar Nijar dan duba sabon sauyin rungumar kana nan sana’oi  da ake gani wajan daliban jami’oin kasar, da nufin samun na kalace ko kuma rufawa kai asiri, kamarsu yankan farshe da kayan gwari da sauransu, sabanin yadda lamarin yake a baya.
Published 03/31/21
Shirin ''Kasuwa a kai miki Dole'' tare da Abubakar Isah Dandago ya mayar da hankali kan mahawarar da ta kaure kan matakin kulle filin jirgin saman Jihar Kano ga masu tafiye-tafiyen ketare na tsawon shekaru.
Published 03/26/21
Yajin aikin hadakar kungiyoyin masu fataucin dabbobi da kayan gwari, da suka ce, sun kira shi ne, saboda rikicin da ya faru a kasuwar SASA dake Ibadan, lamarin da ya kai ga asaran rayuka da dukiyoyi.Kasuwar Mile 12 international dake birnin Lagos, ita tafi jin jiki da tafka asara sakamakon yajin aikin, to sai dai, yanzu haka al’amura sun dan dai-daita bayan dage yajin aiki. A cikin shirin kasuwa a kai miki dole,Ahmed Abba ya duba halin da ake cikin yanzu haka.
Published 03/17/21
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan mako tare da Ahmed Abba ya leka kasuwar alade mafi girma a arewa maso gabashin Najeriya, wato karamar hukumar Numan dake Jahar Adamawa.
Published 03/10/21
Shirin Kasuwa akai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba  ya maida da hankali ne kan nadin da Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO ta yi wa Dakta Ngozi Okonjo Iweala a matsayin shugabanta, Mace ta farko bakar fata kuma 'yar Najeriya da ta taba darewa Kujerar a tarihi.
Published 03/03/21
Shirin Kasuwa akai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya maida hankali ne kan kasuwar hada hadar kudade ta Internet da ake kira Crypto Currency, hada hadar da sannu a hankali ke karade Duniya, ciki harda nahiyar Afrika.
Published 02/10/21
Shirin Kasuwa Akai miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba, ya yada zango ne jihar Yobe dake arewa maso Gabashin Najeriya, inda yayi dubi kan sabbin kasuwannin zamani da gwamnan jihar Maimala Buni ya gina a wasu manyan garuruwan jihar don farfado ta tattalin arzikin jihar dake fama da rikicin Boko Haram.
Published 02/04/21