Halin da 'yan Najeriya ke ciki bayan karin farashin Mai da Lantarki - 09/09/2020
Listen now
Description
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yada zango ne a tarayyar Najeriya, inda mahawara ta kaure a kasar tun bayan matakin kara kudin Litar man fetir dana lantarki, inda a hannu guda kuma jama’a a sassan kasar ke cigaba da maida martani, lura da halin matsin rayuwar da aka tsinci kai sakamakon annobar corona, kuma sai gashi kwatsam an wayi gari da wannan yanayi, wanda galibin al ummar Najeriyar musamman talakawa, ke ganin zai sake jefasu su ne cikin mawuyacin hali kari kan wanda suke ciki.
More Episodes
Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan makon ya tattauna kan yadda matsalar rashin ayyukan dake karuwa tsakanin matasa ke yin tasiri kan sha'anin tsaro da tattalin arziki a Najeriya.
Published 12/02/20
Published 12/02/20
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya yi nazari ne game da zargin ha'inci da ake yi wa masu gidajen man fetur.
Published 11/25/20