Episodes
Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan makon ya tattauna kan yadda matsalar rashin ayyukan dake karuwa tsakanin matasa ke yin tasiri kan sha'anin tsaro da tattalin arziki a Najeriya.
Published 12/02/20
Published 12/02/20
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya yi nazari ne game da zargin ha'inci da ake yi wa masu gidajen man fetur.
Published 11/25/20
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole da wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida hankali ne dangane da wani Shiri na gwamnatin Najeriya na taimakawa mata nakasassu, a kokarin saukakawa al’umma tsananin rayuwa da annobar korona ta haifar, karkashin ma'aikatar jinkai da walwalar al'umma ta kasar.
Published 11/04/20
Shirin Kasuwa akai miki dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya yi duba na tsanaki game da illar da zanga-zangar ENDSARS wadda ta juye zuwa rikici ta haifarwa tattalin arzikin Najeriya, musamman bayanda wasu batagari suka rika amfani da damar wajen balle rumbunan adana abinci tare da yashesu ciki har da na daidaikun 'yan kasuwa baya ga na gwamnati.
Published 10/28/20
Shirin Kasuwa Akai miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba, ya daura kan shirin makon jiya, inda muka duba kalubalen dake tattare da matakin gwamnatin jihar Zamfara na kafa taskar adana Zinari.
Published 10/21/20
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya tattauna ne game da shirin gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya na kafa wani asusun adana zinari domin gina jihar ta fannoni da ...
Published 10/14/20
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole ya yi nazari ne kan wani sabon tsari da Hukumar Alhazan Najeriya ta bullo da shi tare da hadin guiwar Bankin Musulunci na Ja'iz domin bai wa marasa karfi damar tara ...
Published 10/07/20
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yada zangone a jamhuriyar Nijar, inda gwamnatin kasar ta fara rabawa masu karamin karfi tallafi na musamman domin rage kaifin talauci da bullar annobar korona ta jefasu ciki, sakamakon yadda kanana da matsakaitun sana’o’i suka durkushe.
Published 09/30/20
Shirin Kasuwa Akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya duba yadda sabon Doya ya kawo saukin farashin kayayyakin abinci a jihar Adamawa dake Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Published 09/23/20
A cikin shirin 'Kasuwa A Kai Miki Dole', Ahmed Abba ya duba irin tallafin da hukumomin Najeriya suka baiwa kanana da matsakaitan sana'o'i da suka durkushe dalilin annobar COVID 19, da kuma yadda kwararru ke kallon shirin na gwamnati.
Published 09/16/20
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yada zango ne a tarayyar Najeriya, inda mahawara ta kaure a kasar tun bayan matakin kara kudin Litar man fetir dana lantarki, inda a hannu guda kuma jama’a a sassan kasar ke cigaba da maida martani, lura da halin matsin rayuwar da aka tsinci kai sakamakon annobar corona, kuma sai gashi kwatsam an wayi gari da wannan yanayi, wanda galibin al ummar Najeriyar musamman talakawa, ke ganin zai sake jefasu su ne cikin mawuyacin hali...
Published 09/09/20
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankalin ne kan yadda cutar korona ta kassara tattalin arzikin kasashen duniya, masamman tarayyar Najeriya.
Published 08/19/20
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba, ya yi nazari kan wani shirin gwamnatin Najeriya na samar da aiyukan yi ga matasan kasar samada dubu dari bakwai, shirin da ake saran zai baiwa matasa dubu daya aiki a kowacce karamar hukuma dake fadin kasar.
Published 08/12/20
Shirin Kasuwa Akai miki Dole na wannan makon ya duba kasuwar musayar kudin kasa da kasa ne a Tarayyar Najeriya, inda kudin kasar na Naira ke cigaba da faduwa, yayin da kimar kudaden kasashe ketare ke tashin gwaron-zabi. Wannan faduwar na darajar kudin Naira a cewar masana, na cigaba da haddasa mummunan tasiri a tattalin arzikin kasar, tare da haifar hauhawan farashin kayayyakin masarufi.
Published 08/05/20
Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmad Abba, ya duba hada-hadar kasuwannin dabbobin Layya a jamhuriyar Nijar da Tarayyar Najeriya, gabanin babbar salla ko sallar Layya dake tafe ...
Published 07/29/20
Gwamnatin Najeriya,ta bullo da wani tsari don daina dogaro da arzikin man feutr,hakkan ya sa hukumomi mayar da hankali tareda neman bunkasa bangaren noma. Bincike ya nuna cewa wasu daga cikin ...
Published 07/08/20
Shirin Kasuwa akai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba, ya maida hankali ne kan kanana da matsakaitun masana’antu, wanda alkaluman hukumar kasuwanci ta duniya ke nuna su ke da kashi 90 na harkokin kasunci da ke gudana a fadin duniya, kuma suke samar da kashi 70 na ayyukan yi, kana suke samar da kashi 50 na tattalin arzikin a ma’aunin GDP, da kuma yadda matasa ke dogaro da kai a Najeriya.
Published 07/01/20
Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi duba kan dimbin nasarori da gwamnatin Najeriya ta samu a bangaren sufurin jiragen ruwa, wanda shikadai ke aiki tun bayan dakatar da sauran harkokin sufurin tsakaninta da wasu kasashe saboda barkewar cutar coronavirus.
Published 06/24/20
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida hankali  kan yadda jama’a da dama ke fadawa tarkon ‘yan damfara da sunan tallafi ko agajin gwamnati don rage radadin dokar kulle don hana yaduwar cutar korona masamman a Tarayyar Najeriya.
Published 06/10/20
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wanna lokaci yayi duba matsalar da ta kunnowa 'yan Najeriya kai ne ta tashin gauron zabin farashin kayan masarufi, a daidai lokacinda da jama'a ke fama da tasirin annobar coronavirus da ta tsayar da hada-hadar kasuwanci da tilasta yiwa mutane kulle a gida.
Published 05/13/20
Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan lokaci yayi nazari kan yadda kasuwar dinki da kuma sayar da takunkumin rufe baki da hanci ta yi karfi a kasashen duniya, musamman Najeriya, saboda dakile annobar coronavirus.
Published 05/06/20
Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba, yayi tattaki zuwa jihar Kano, inda ya duba halin da al'ummar jihar suka shiga bayan soma aikin dokar hana fitar da gwamnati ta kafa, domin dakile yaduwar annobar coronavirus.
Published 04/22/20
Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole wannan mako tare da Ahmed Abba ya tattauna ne kan yadda Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya tallafa wa miskinai da kayyakin abinci da kudade a daidai wannan ...
Published 04/15/20