Episodes
Shirin "Kasuwa a kai miki Dole" na wannan makon ya daura ne kan shirin makon da ya gabata, wanda ya mayar da hankali kan halin yadda batun tsarin kudin Fansho yake a tarayyar Najeriya, la'akari da irin matsalolin da masu karbar fansho ko iyalansu suke fuskanta a kasar.
Published 03/25/20
Shirin "Kasuwa a kai miki Dole" na wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin nazarin yadda batun tsarin kudin Fansho yake a tarayyar Najeriya, la'akari da irin matsalolin da masu karbar fansho ko iyalansu suke fuskanta a kasar.
Published 03/18/20
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannnan mako tare da Ahmed Abba, ya maida hankali ne kan matakin gwamnatin jihar kaduna dake Najeriya na rusa kasuwar barci dake jihar a kokarin sake fasalin zamanantar da kasuwanni birnin Kaduna daga yadda suke, matakin da ya tada hankalin 'yan kasuwa da al'ummar birnin.
Published 03/11/20
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi nazari ne kan alkaluman d Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar da ke cewa, an samu tashin farashin kayayyakin masarufi a ...
Published 03/04/20
A cikin shirin na wannan lokaci Ahmed Abba ya duba batun shirin gwamnatin Najeriya na samar da ayyukan yi ga matasan kasar, musamman yadda Gwamnatin ke ci gaba da zaburar da masu hannu da shuni wajen ...
Published 02/26/20