Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Shugaba Biya na Kamaru ya fara daukan matakan sulhu da abokan hamayya
Listen now
Description
A kokarinsa na sulhunta bangarorin kasar, shugaban Kamaru Paul Biya, ya saki jagoran adawar kasar Maurice Kamto da wasu magoya bayansa, da kuma wasu ‘yan aware da ke tsare a kurkuku, ba tare da shugabannin su ba. kungiyoyin kare hakkin bil’adama irinsu Amnesty International da sauran su, sun bayyana hakan a matsayin matakin farko na kawo karshen musgunawa ‘yan adawa a kasar. Ku yaya kuke kallon wannan mataki? Wace hanya kuke ganin ya kamata abi wajen sulhunta bagarorin kasar Kamaru, bayan tsawon watanni ana rikici da juna?