Episodes
Shirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan rana tare da Nasiri Sani ya baku damar tofa albarkacin bakinku ne dangane da shigar da jamhuriyar Nijar ta yi cikin jerin kasashen da suka tilastawa jami’an aikin lafiya da kuma daliban su karbar allurar rigakafin cutar korona domin dakile yaduwar ta.
Published 11/24/21
Shirin 'Ra'ayoyin masu Sauraro' tare da Hauwa Aliyu ya tattauna ne kan ranar 23 ga watan Yunin wacce Majalisar Dinkin Duniya ta ware wa matan da mazajensu suka mutu, da nufin nazari kan kalubalen da ke addabarsu da kuma magance musu shi, tare da kare musu hakkokin su. An kiyasta cewa matan da mazajensu suka mutu a fadin duniya sun haura miliyan dari biyu da hamsin da takwas, inda da dama daga cikin su ke cikin ukuba ta rayuwa.
Published 06/23/21
Shirin Ra'ayoyin masu sauraro na wannan mako ya bada damar tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi rayukansu ta fuskokin tsaro, tattallin arziki, Siyasa da kuma zamantakewa.
Published 09/18/20
Hukumar Lafiya ta Duniya tayi shelar cewar Afirka ta rabu da cutar polio bayan kwashe dogon lokaci ana yaki da cutar a fadin duniya. Hukumar tace tayi nasarar kare yara miliyan guda da dubu 800 daga zama guragu, yayin da ceto rayukan mutane 180,000 wajen yaki da cutar. Yaya kuke kallon wannan nasara? Wane irin darasi ya dace Afirka ta koya daga wannan yakin ? Ta yaya kuke ganin Afirka zata yaki wasu cututtukan da suka rage ?
Published 08/26/20
Hukumar zaben Jamhuriyar Nijar, ta ce ba za ta iya gudanar da zabe domin bai wa ‘yan kasar dake zaune a kasashen ketare damar samun wakilci a Majalisar dokokin kasar ba, sannan kuma ba za ta iya gudanar da zaben kananan hukumomi ba duk da cewa wa’adinsu ya kawo ya kawo karshe. A baya dai cikin watanni masu zuwa aka tsara gudanar da sabbin zabuka a kasar ta Nijar, sai dai hukumar zabe ta ce ba ta da lokacin yi wa masu kada kuri’u rijista a kasashen ketare, matakin da tuni ya samu amincewar...
Published 06/30/20
Shirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan rana tare da Zainab Ibrahim, ya tattauna ne dangane da matakin shugaban Najeriya Mohammadu Buhari kan janye shirin sakarwa majalisun jihohi da bangaren shari'a mara, mako guda bayan sanya hannu akan dokar da zata tabbatar da hakan, bayan ganawa da shugaban ya yi da tawagar Gwamnonin kasar wadanda ke adawa da shirin, duk kuwa da farin cikin da ‘yan Najeriya suka bayyana a kan matakin.  
Published 06/10/20
Kwamandan rundunar sojin Amurka ta Africon general Stephen Townsend ya bayyana rashin gamsuwa da yadda kasashen turai ke yaki da yan ta’adda a sahel ba tare da tsari mai kyau ba. Duk da kudade da sojoji da kayan yaki da wadannan kudade suke zubawa. kwamandan ya ce wadannan mayaka suna barazana ne ga turai sabanin Amurka. Kuna kallon wadan nan kalamai a matsayin yunkurin Trump na janye dakarun sa zuwa gida?
Published 03/12/20
Shirin ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan lokaci tare da Zainab Ibrahim, ya tattauna matakin Majalisar Dattawan Amurka na kada kuri’ar kin amincewa da matakin kiran masu bada shaida da kuma tattara sabbin hujjoji dangane da tsige shugaban kasar Donald Trump. Ana ganin matakin da Majalisar Dattawan mai rinjayen ‘yan Jam’iyar Republican ta dauka, zai kai ga wanke Trump daga zarge-zargen amfani da karfin ikonsa ta hanyar da ba ta dace ba. Tuni Majalisar Wakilan kasar ta tsige shugaban daga...
Published 02/03/20
Shirin ra'ayoyin masu saurare ya tattauna kan matakin kasashen yammacin Afrika 8 renon Faransa, da suka amince da sauya sunan takardar kudin da suke amfani da ita a hukumance daga CFA zuwa Eco, a daidai lokacin da kungiyar kasashen yammacin Africa ke shirin samar da kudin bai - daya mai suna ECO, lamarin da ake ganin riga – malam masallaci ne ga shirin na ECOWAS.
Published 12/23/19
Taron shugabannin kasashe 5 na yankin Sahel da ya gudana ranar lahadi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, ya jaddada muhimmancin ci gaba da hulda da kasashen duniya don yaki da ta’addancin a yankin na Sahel. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da, a wasu kasashe aka fara nuna shakku dangane da irin rawar da dakarun kasashen yammacin duniya ke takawa a wannan yaki. Menene ra’ayoyinku game da amfani ko rashin amfani dakarun kasashen ketare a wannan yaki? Anya yankin Sahel zai iya tabbatar...
Published 12/17/19
Kungiyar agajin kasar Faransa ta Action Against Hunger ta sanar da kashe jami’an ta guda 4 da kungiyar Boko Haram tayi garkuwa da su tun a watan Yuli. Kisan ya gamu da suka daga Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma kungiyar agajin dake taimakawa mutane 300,000 da rikicin Boko Haram ya tagayyara. Kan wannan batu muka baku damar tattaunawa a wannan litinin.
Published 12/16/19
Shirin ra'ayoyin maso sauraro kowace Jumma'a na bada damar tofa albarkacin bakin kan duk wasu batutuwa da ke cimmuku tuwo a kwarya, a wannan karon ma masu saurararo sun bayyana ra'ayoyin su kan batutuwa da dama.
Published 11/22/19
Shirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan lokaci tare da Zainab Ibrahim,ya tattauna kan yawaitan hare-haren ta'addanci a sansanonin sojin kasar Mali, wanda ake ganin ya hallaka dakarun Mali sama da 100, duk kuma da cewa akawi dakarun G5 Sahel da na kasashen waje a kasar.
Published 11/21/19
Shirin Ra'ayoyin Masu Sauraro na wannan ranar ya bada damar yin tsokaci ne kan ranar bandakuna ta duniya, ranar da ake karfafa wayar da kan jama'a kan yakar yin bahaya a bainar jama'a. Bikin na bana yazo ne yayinda majalisar dinkin duniya ta ce sama da mutane biliyan 3 ke rayuwa cikin rashin tsaftar muhalli.
Published 11/19/19
Majalisar dokokin Najeriya ta gabatar da kudirin dokar hukunta duk wanda aka kama da laifin yada kalaman kiyayya, da daurin shekaru 10 a gidan yari ko biyan tarar naira miliyan 10. Matakin ya haifar da suka daga bangarorin adawa, alkalai da kuma kungiyoyin fararen hula, inda suka ce kudurin dokar ya yi tsanani. Kan wannan al'amari a wannan karon muka baiwa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyi akai.
Published 11/14/19
Kamar yadda wata kila kuka ji a cikin labaran duniya, shugaban kasar Bolivia Evo Morales ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon takkadamar da ta biyo bayan sake nasarar zabensa, wanda yasa sojan Kasar da ‘Yan sanda janye goyon baya da suke bashi. Gwamnatin Bolivia ta bayyana shirinta na sake gudanar da sabon zabe dan kawo karshen rikicin siyasar Kasar. Kan wannan batu muka baku damar tofa albarkacin baki, a wannan rana ta talata 12 ga Nuwamban 2019.
Published 11/12/19
Kasashen duniya na ci gaba da bayyana farin ciki kan samun nasarar kashe shugaban kungiyar mayakan IS, Abubakar al-Baghadadi da dakarun Amurka suka yi saboda illar da ya yiwa duniya. Sama da Kasashe 30 dake yaki da kungiyar na shirin ganawa a ranar 14 ga watan nuwamba dan cigaba da neman Karin goyan baya daga abokan su wajen yaki da ta’addanci. Kan wannan batu muka baiwa masu sauraro damar tofa albarkacin bakinsu.
Published 10/30/19
A kokarinsa na sulhunta bangarorin kasar, shugaban Kamaru Paul Biya, ya saki jagoran adawar kasar Maurice Kamto da wasu magoya bayansa, da kuma wasu ‘yan aware da ke tsare a kurkuku, ba tare da shugabannin su ba. kungiyoyin kare hakkin bil’adama irinsu Amnesty International da sauran su, sun bayyana hakan a matsayin matakin farko na kawo karshen musgunawa ‘yan adawa a kasar. Ku yaya kuke kallon wannan mataki? Wace hanya kuke ganin ya kamata abi wajen sulhunta bagarorin kasar Kamaru, bayan...
Published 10/07/19