Episodes
Ra'ayoyin masu sauraro na wannan rana tare da Zainab Ibrahim ya tattauna kan matakin babban bankin Najeriya CBN na karin harin masu ajiya da kuma fitar da kudin a bankunan kasar.
Published 09/19/19
Shirin Ra'ayoyin Masu Sauraro na wannan rana ta Juma'a, kamar yadda aka saba ya bada damar tattaunawa da jan hankalin hukumomi kan muhimman batutuwan da ke damun al'umma.
Published 07/12/19
Shirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan ranar tare da Micheal Kuduson, ya tattauna ne kan ranar 11 ga watan Yuli da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar yawan al'umma ta Duniya, domin yin nazari kan batutuwa da yawan jama'a kan janyo domin magance wa.  
Published 07/11/19
A kowace ranar Jumma'a shirin ra'ayoyin masu saurare kan baku damar tofa albarkacin bakin ku kan duk wani maudu'in da ke cimmu ku tuwo a kwarya.
Published 06/28/19
Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan ranar tare da Zainab Ibrahim, ya tattauna ne kan matakin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron kan shirin rufe tashoshin samar da makamashin nukiliyar kasar 14 daga cikin 58 da suke da shi nan da shekarar 2035.
Published 11/28/18

Kamar yadda watakila kuka ji a labaran duniya, bayan kwashe tsawon watanni na kokarin cimma yarjejeniya, yanzu haka Kungiyoyin Kwadagon Najeriya sun cimma matsaya da gwamnatin kasar kan mafi karancin albashin ma’aikata. Menene ra’ayoyinku kan tsawon lokacin da aka dauka na cece-kuce tsakanin bangarorin biyu kan wannan batu? Ko kuna ganin cewa, shugaba Buhari zai amince da dogon yajin aiki a dai dai lokacin da zabe ke karatowa? Shin kuna ganin yajin aiki na taka muhimmiyar rawa wajen...
Published 11/06/18
Kamar yadda watakila kuka ji a labaran duniya, bayan kwashe tsawon watanni na kokarin cimma yarjejeniya, yanzu haka Kungiyoyin Kwadagon Najeriya sun cimma matsaya da gwamnatin kasar kan mafi karancin albashin ma’aikata. Menene ra’ayoyinku kan tsawon lokacin da aka dauka na cece-kuce tsakanin bangarorin biyu kan wannan batu? Ko kuna ganin cewa, shugaba Buhari zai amince da dogon yajin aiki a dai dai lokacin da zabe ke karatowa? Shin kuna ganin yajin aiki na taka muhimmiyar rawa wajen magance...
Published 11/06/18
Kowacce Ranar 16 ga watan Oktoba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ke warewa a matsayin ranar samar da abinci ta duniya. Taken bikin na bana dake gudana a birnin Geneva shi ne ‘Ana iya magance yunwa a duniya.’ Shirin Ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan lokaci, ya baku damar tofa albarkancin bakinku kan yadda harkar noma da samar da abinci ke gudana a yankunan ku.
Published 10/16/18

Shirin Ra'ayoyin Masu Sauraro na wannan lokacin, ya bada damar tofa albarkacin baki ne kan dambarwa dake neman kunno kai a zaben kasar Kamaru, inda dan takara daga jam’iyyar adawa, Maurice Kamto ke ikirarin lashe zaben shugabancin kasar, gabanin fitar da sakamakon hukumar zabe. Sai dai gwamnatin kasar ta yi watsi da ikirarin na Kamto tare da jan kunnensa.
Published 10/09/18

Kamar yadda wasu suka samu saurara a labarun duniya da sashin Hausa na RFI ya watsa, a makon jiya ne makarantun boko a Jamhuriar Nijar da suka hada da jami'o'i suka koma bakin aiki bayan janye yajin aikin da suka tsunduma. Matsalar yajin aiki na haifar da cikas ga bangaren ilimi a Nijar, lura da cewa kusan kowacce shekara sai malamai sun gudanar da ita. Shirin ra'ayoyin ku asu sauraro ya baku damar tofa albarkancin bakinku ne akan yadda za a shawo kan wannan matsala.
Published 10/03/18

Ra'ayoyin masu saurare, kan sanin ko kasancewar kasar china a kasuwanin nahiyar Afrika wani sabon salon  mulkin mallaka ne, ta hanyar damfarawa kasashen nahiyar bashi kamar yadda kasashen yammaci ke fada, haka ne ko kuma a a. Ga dai ra'ayin wasu daga cikin masu saurare tare da Zainab Ibrahim
Published 09/25/18

hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya ta ce yanzu haka rabin makarantun duniya basu da tsaftatacin ruwan sha, da kuma bandaki, tare da wajen wanke hannu. Al'amarin da majalisar dinkin duniyar ta yi gargadin cewa, na barazana ga koshin lafiyar yara da kuma malamansu. Ga dai ra'ayoyin wasu daga cikin masu saurare kan wannan rahoto, a tattaunawar da ta hada su da Zainab Ibrahim.
Published 08/28/18

A yau ne al'umar musulmi suka gudanar da shagulgulan  sallar layya a kasar jamhuriyar Nijer. Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya baiwa wasu daga cikin masu saurarenmu damar isar da barka da sallarsu ga yan uwa da abukan arziki a kasar, tare da Zainab Ibrahim.
Published 08/22/18

Shirin Ra'ayoyin Masu Sauraro na wannan lokaci, ya bada damar tattaunawa ne kan bangarorin siyasar da ba sa ga maciji da juna a Sudan ta Kudu, a karo na karshe, sun sanya hannu a kan yarjejeniyar raba madafun iko a kasar Sudan, wanda ake sa ran za ta haifar da kafa Gwamnatin hadin kai, kowane bangare kuma zai bada gudumawar Ministoci da ‘yan Majalisu.
Published 08/06/18

Shirin ra'ayoyin masu saurare tare da Zainab Ibrahim ya baku damar tofa albarkacin baki kan dawowar madugun 'yan tawayen Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Jean Perri Bembe gida kinshasa a jiya Laraba.
Published 08/02/18