Mace 1 cikin masu juna biyu 95 na mutuwa yayin haihuwa a jihar Neja - bincike
Listen now
Description
Shirin Lafiya Jari a wannan makon zai yi duba ne kan binciken wata cibiyar bin diddigi kan harkokin kiwon lafiya ta Nigeria Health Watch wanda ya nuna cewa mace daya cikin masu juna biyu 95 na mutuwa a lokacin haihuwa a jihar Neja ta arewacin kasar, lamarin da ake ganin akwai sakaci na al'umma da kuma rashin kulawar hukumomin kula da lafiya a jihar ta fannin samar da kwararrun ma'aikata a dukkanin asibitocin jihar.  
More Episodes
Shirin na wannan mako ya duba yadda kananan yara musamman a Najeriya da sauran kasashe masu tasowa ke gaza karbar alluran rigakafin da ya kamata su samu kafin cika shekaru biyar da haihuwa.
Published 05/27/24
Published 05/27/24
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya yi duba ne a kan halin da ake ciki a yaki da cutar Tamuwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar.
Published 05/20/24