Yadda hanyoyin gargajiya ke samun karbuwa wajen magance cutar sikila
Listen now
Description
Shirin 'Lafiya Jari Ce'  na wannan mako ya yi nazari ne kan hanyoyin gargajiya da ake bi wajen magance cutar  sikila  da kuma yadda al'umma suka karbi wadannan hanyoyi don samar wa kansu mafita. Shirin ya tattauna da masu maganin gargajiya da ke ikirarin cewa magungunansu na samar da waraka, kana ya gana da  liitocin zamani don neman karin haske a kan inda aka kwana wajen neman mafita a game da wannan cuta ta sikila. 
More Episodes
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya duba yanayin lafiyar mahajjata, a dai-dai lokacin da al'ummar Musulmai ke gudanar da ibadar hajji a Saudiyya.
Published 06/10/24
Published 06/10/24
Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan yadda har yanzu wasu daga cikin al’ummar Najeriya basa amfani da tsarin inshorar lafiya. A shekarar 2022 ne gwamnatin kasar ta sake dawo da dokar inshorar lafiya da aka samar tun 1999, a wani yunƙuri na sauƙaƙawa Jama’a samun kulawar lafiya...
Published 06/03/24