Yawaitar gurbatattun jami'an lafiya a asibitocin Najeriya
Listen now
Description
A wannan makon shirin ya mayar da hankali kan yawaitar gurbatattun jami’an lafiya a asibitocin Najeriya wanda ke da nasaba da kodai rashin samun cikakken horo a kwalejojin lafiya ko kuma samun horon irin wadannan makarantu amma na bogi. A baya-bayan nan ana yawan ganin yadda ake bude tarin makarantu masu zaman kansu a sassan Najeriya da sunan horar da jami’an lafiya kama daga kwalejoji har da jami’o’I wadanda wasu daga cikinsu kan rasa sahalewar mahukuntan saboda rashin cancanta.
More Episodes
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya duba yanayin lafiyar mahajjata, a dai-dai lokacin da al'ummar Musulmai ke gudanar da ibadar hajji a Saudiyya.
Published 06/10/24
Published 06/10/24
Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan yadda har yanzu wasu daga cikin al’ummar Najeriya basa amfani da tsarin inshorar lafiya. A shekarar 2022 ne gwamnatin kasar ta sake dawo da dokar inshorar lafiya da aka samar tun 1999, a wani yunƙuri na sauƙaƙawa Jama’a samun kulawar lafiya...
Published 06/03/24