Episodes
daruruwan dubban mutane ne ke mutuwa sanadiyar kwankwadar gurbatacen magani a duniya, al'amarin dake ci gaba da saka ciwon kai, ga mahukumta dake ta kokarin ganin sun magance matsalar bazuwa magungunnan jabu a duniya, a kan haka cikin shirin Azima Bashir Aminu ta duba mana yadda matsalar ta yi kamari a kasar Kamaru.
Published 08/14/23
Shrin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako zai mayar da hankali ne a kan cutar rashin bacci, ko kuma rashin samun baccin a lokacin da ake bukata.  Alkalumma sun nuna cewa kashin 30 zuwa 35 na al'ummar duniya, wadanda shekarunsu ya kai 18 zuwa sama na fama da wannan cuta ta rashin samun isassehn bacci wadda ake kira insomnia a turance. Shirin ya tattauna da kwararren likita, wanda ya yi bayani a game da wannan cuta da ta addabi al'umma.. 
Published 07/31/23
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar Down Syndrome ko kuma Galahanga, cutar da har yanzu al'umma ke da karancin sani kan yadda za su kula da masu fama da ita.
Published 07/17/23
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba kan tsanantar cutar Typhoid a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya, wanda masana ke alakantawa da gurbatar ruwan da jama'a ke ta'ammali da shi yayin hada-hadar yau da kullum.
Published 07/11/23
Shirin Lafiya jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya dora akan maudu'in makon da ya gabata wato amtsalar nan ta kaurar likitocin matalautan kasashe irin Najeriya zuwa manyan kasashe.
Published 07/03/23
Shirin 'Lafiya Jari ce' a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu, ya tabo babban kalubalen da bangaren lafiya ke fuskan ne a kasashen Afrika, na yadda tarin kwararrun likitoci ke ci gaba da yin kaura daga kasashen zuwa Turai ko Amurka da nufin samun ingantacciyar rayuwa, batun da ke ci gaba da kassara bangarorin lafiyar nahiyar. Najeriya ke matsayin kan gaba a yawan likitocin da ke barin kasar a kowacce rana zuwa ketare.  
Published 06/26/23
Shirin 'Lafiya Jari ce' a wannan makon ya yi nazari ne gameda yadda mahajjaci ya kamata ya kula da lafiyarsa a yayin da ya ke kasa mai tsarki, don samun damar yin ibadar da ta kaishi yadda ya kamata.
Published 06/19/23
Shirin lafiya jari na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan cutar bugawar zuciya ko kuma Heart Attack a turance, cutar da kididdiga ke nuna cewa yanzu haka akwai mutane fiye da miliyan 200 da ke fama da ita a sassan Duniya.
Published 06/05/23
Shirin na wannan mako zai maida hankali ne kan cutar makero, guda cikin cutukan fatar da ke matsayin ruwan dare a wannan lokaci musamman tsakanin kananan yara. 
Published 05/29/23
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar karkarwar jiki ko kuma Parkinson a turance wadda wasu ke alakantawa da yawan shekaru, inda a yanzu haka ake da jumullar mutane fiye da miliyan 10 da ke fama da ita.
Published 05/22/23
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan karuwar masu fama da cutar tarin fuka ko kuma TB da ke ganin bazuwarsa a sassan Najeriya duk kuwa da gangamin yaki da cutar da gwamnatoci ke yi.
Published 05/15/23
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya duba yadda matsalar sauya wasu takardun kudin Nairar Najeriya da tsadar rayuwa suka shafi harkokin asibiti masamman majinyata ko masu bukatar gaggawa a asibiti.
Published 04/10/23
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutukan da ke tasiri a lokacin azumun watan Ramadan dama nau'ikan abincin da ya kamata masu irin cutukan su rika ma'amala da su.
Published 04/03/23
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda wasu asibotoci a Jamhuriyyar Nijar ke fama da karancin jini sakamakon rashin masu bayar da gudunmawar jinin don tallafawa marasa lafiya.
Published 03/27/23
Shirin "Lafiya jari ce"  na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsalar shaye-shaye sannu a hankali ke ci gaba da jefa tarin matasa a lalurar hauka ko kuma tabin hankali, matsalar da ke ci gaba da tsananta a sassan Jamhuriyya Nijar musamman tsakanin matasa ko kuma daliban jami’o’i.  Alkaluman ma’aikatar lafiyar Nijar na nuna yadda ake da tarin matasa da yanzu haka ke karbar maganin cutar kwakwalwa galibinsu sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi ko kuma shaye-shayen zamani. 
Published 03/13/23
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wanna mako ya kawo mana yadda jama'a za su duba lafiyarsu ne a lakcin zabuka. Wannnan maudu'i na zuwa ne bisa la'akari da yadda jama'a da dama suka samu rauni, wasu kuma suka mutu saboda tarzomar da  ta tashi a lokacin zaben shugaban kasa a Najeriya.
Published 03/06/23
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan lokaci ya tattauna akan cutar Gout da ke kumbura sassan jikin Dan Adam ciki kuwa har da jjijiyoyi.
Published 02/20/23
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar farfadiya ko kuma Epilepsy a turance, cutar da ke matsayin babbar barazanar lafiya ga jama'a musamman a kasashe masu tasowa da ke karancin kulawar lafiya.
Published 02/13/23
Shirin lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba wani ci gaban lafiya da aka samu a Najeriya bayan da hadaka tsakanin ma'aikatar lafiya da hukumar sadarwa ya kai ga samar da wata manhaja wadda za ta saukakawa marasa lafiya samun damar ganin likita tun gabanin su je asibiti, a wani yunkuri na dakile cunkoson da ake samu a asibitocin kasar.
Published 02/06/23
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan ci gaban lafiyar da aka samu a jihar Yobe a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, bayan da gwamnatin jihar ta samar da sabbin asibitoci da kuma horar da malaman jinya don dakile matsalolin lafiyar da jihar ke fuskanta.
Published 01/30/23
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi nazari ne kan sake bazuwar cutar kuturta a Najeriya, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kasar ce ke kan gaba wajen yawan kutare a kasashen Afrika.
Published 01/23/23
A Najeriya ana ci gaba da samun matsalar cutar sankarar mama, cutar d har yanzu babu takamammen maganinta duk kuwa da cewa daya bisa uku na matan duniya na cikin hadarin kamuwa da ita. Har yanzu dai kwararru sun gaza gano aininhin abin da ke haddasa wannan cuta, sai dai sun ce sun gano dalilan da suka sa take kama wasu nau'ukan mata fiye da wasu.
Published 11/28/22
Shirin 'Lafiya Jari ce' ya mayar da haankali ne a kan yadda mutane ke boye cutukan da ke damunsu har  su kai ga ta'azzara a jikinsu, musammam cutukan da suka shafi kwakwalwa. sau da damu a cikin al'ummarmu, mutane ba sa zuwa ganin likitan kwakwalwa, ko kuma kaai 'yaan uwansu, don kawai kada a danganta su da laallurar tabin hankali.
Published 10/31/22
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda cutar tamowa ko kuma yunwa sakamakon rashin abincin mai gina jiki ke kashe yara miliyoyin kananan yara duk shekara inda a baya-bayan nan wasu alkaluman MSF ke nuna yadda kusan kashi 50 na yaran arewacin Najeriya ke fama da wannan cuta. Ayi saurare Lafiya.
Published 10/24/22
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna da kwararru kan wani rahoto da ya bayyana cewar, fiye da kashi 67 na mata a Najeriya, na fama da matsalar karancin jini. 
Published 10/17/22