Episodes
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako tare da  Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda zaman kotun sauraron korafe-korafe kan likitoci ya gudana, a wani yunkuri da hukumar kula da ayyukan likitoci ta Najeriya ke yi don magance yawan sakacin da likitocin ke yi a bakin aiki.
Published 12/13/21
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon, ya yi dubi ne da sabon nau'in cutar Covid-19 na Omicron da aka fara ganowa a kasar Afirka Ta Kudus. Azima Bashir Aminu ce ta shirya ta gabatar, tare da taimakon wakilinmu na Bauchi an Najeriya Ibrahim Malam Goje.
Published 12/06/21
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon ya tattauna da masana akan yadda magungunan da aka sarrafa daga itatuwa da nau'ikan kayan abinci ke samun karbuwa a tsakanin mutane.
Published 11/29/21
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali kan wani shirin inganta lafiyar kananan yara a yankin arewa maso gabashin Najeriya bisa hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross da gwamnatin jihar Adamawa wanda ya kai ga samar da wata manhajar duba yara tare da lalubo lalurar da ke damunsu. Ayi saurare Lafiya. 
Published 11/22/21
Shirin 'Lafiya Jari Ce' a wannan makon ya duba batun illolin cutar sukari ko kuma diabetes a turance, cutar da bisa al’ada ake gudanar da bikin yaki da ita a kowacce ranar 14 ga watan Nuwamba a wani yunkuri na wayar da kan jama’a game da illolinta dama yadda za a kare kai daga kamuwa da ita.
Published 11/15/21
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu na wannan mako, ya yi duba kan yadda cutar tsananin damuwa kan kisan miliyoyin mutane ba tare da sani ba, cutar da WHO ke cewa ta na barazana ga rayukan mutane musamman a nahiyar Afrika
Published 11/09/21
A cikin shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako, Azima Bashir Aminu ta yi nazari ne a kan mahimmancin duba lafiya akai akai, inda masana harkar lafiya suka shawarci al'umma da su rika duba lafiyarsu akalla sau 3 a shekarar.
Published 10/11/21
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu, ya tattauna kan rahoton binciken wani kwararren likita biodun Salami  da yayi fice wajen gwajin kwayar halittar Bil Adama a Najeriya, wanda ya ce daga cikin yara 10 da ake gabatar musu domin yin gwaji, 6 daga cikin su ba mutanen da ake zaton iyayen su ne suka haife su ba.
Published 09/27/21
Shirin 'Lafiya Jari ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya duba bayanai dake nuna yadda aka bar Najeriya da wasu kasashe masu tasowa galibi daga nahiyar Afrika a sahun baya ta fuskar bayar da tallafin jinni a asibitoci.
Published 09/20/21
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan yadda masu fama da lalurar laka ke rayuwa da kuma kalubalen da su ke fuskanta dai dai lokacin da Duniya ke ware kowacce ranar 5 ga watan Satumba don wayar da kai kan matsalar.
Published 09/13/21
Shirin wannan mako zai yada zango ne a tarayyar Najeriya inda gwamnatin kasar ta kara fidda sabon salon wayar da kan al’umma game da tabbatuwar annobar Corona, da kuma rungumar allurar rigakafin ta. Wannan ce ta sa gwamnatin ta yi hadin gwiwa da wasu da kungiyoyin mata don taka irin tasu rawar game da fatattakar cutar a kasar a wani taro da hukumar lafiya matakin farko ta shirya d kungiyar mata mai taken MUM. Rukayya Abba Kabara ce ta jagoranci shirin a yau.
Published 08/16/21
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu, ya tattauna kan yadda al'umma masamman a kasashe masu tasowa ke kin amincewa da karbar allurar rigakafin annobar korona.
Published 07/19/21
Shirin 'Lafiya Jari Ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya duba fagabar da al'umma a Najeriya suka shiga sakamakon sake bayyanar cutar Polio ko Shan'inna a wasu sassan kasar, shekara guda bayan da Hukumar lafiya ta Duniya ta wanke kasar daga wannan cuta.
Published 07/12/21
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya maida hankali kan yadda iyaye mata ke yin sakaci wajen shayer da jariransu nonon uwa, inda suke maye gurbinsa sa nau'ukan abincin gongoni.
Published 07/05/21
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda majinyata daga Najeriya musamman masu rike da madafun iko kan tsallake asibitocin cikin kasar tare da balaguro wasu kasashen don duba lafiyarsu, lamarin ake dangantawa da sake tabarbarewar harkokin kula da lafiya a ilahirin asibitocin gwamnatin kasar.
Published 06/21/21
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya cigaba ne kan tattauna halin da ake ciki a jihar Bauchin Najeriya inda hukumomi ke kokarin dakile yaduwar cutar amai da gudawa ko kuma Cholera wadda aka samu bullarta a sassan Jihar.
Published 06/14/21
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya zango a jihar Bauchin Najeriya inda hukumomi ke kokarin dakile yaduwar cutar amai da gudawa ko kuma Cholera wadda aka samu bullarta a sassan Jihar.
Published 06/07/21
Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon ya mayar da hankali kan matakan da Jamhuriyyar Nijar ke dauka a yaki da zazzabin cizon sauro ko kuma Malaria ta hanyar rabon gidan sauro ko kuma sange ga al'ummarta da nufin karesu daga cizon sauron wanda zazzabinsa ke kashe mutane fiye da dubu 5 kowacce shekara a sassan kasar.
Published 05/31/21