Episodes
A wannan zamani da mutum zai iya samun bashi kaitsaye ta waya daga manhajoji daban-daban amma idan mutum ya kasa biya kamfanonin bada bashin kan aika sakonnin cin zarafi da barazana har ga ‘yan uwan wanda ya ci. Duk da gargadin da hukumomi mutane da dama na kukan ana ɓata musu suna, kuma an kasa kulle irin wadannan manhajoji kamar yadda aka ce. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan lamarin, da kuma matakin da mutum zai iya dauka idan kamfanin cin bashi suka bata masa suna.
Published 05/17/24
Gwamnatin tarayyar ta ce za a ɓullo da tsarin auna ƙwazon ma’aikata bisa mizani ta yadda dagewar ma’aikaci zai sa ya samu ƙarin girma ko albashin ma zai iya bambanta, wato dai iya kwazonka iya albashinka. Irin wannan yunkuri na gwamnatin tuni ma’aikata da ‘yan kwadago suka fara suka da tunanin wata manufa ce ta kauda hankali. Toh ko ta fannin shari’a hakan na da tasiri wajen hakkin ma’aikata?  Shirin Najeriya a Yau ya tattauana kan wannan batu.
Published 05/16/24
Published 05/16/24
A baya-bayan nan mazauna manyan biranen Najeriya na ta kokawa game da yadda masu gidajen haya ke neman mai da su saniyar tatsa  wajen tsuga kudin haya. Sai dai masu gidajen na cewa ana fama da tsadar rayuwa kuma kula da irin wadannan gidaje na cin kudi sosai. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan  yadda lamarin ke shafar rayuwar mutanen da  suke zaune a gidajen haya.
Published 05/14/24
Takaddama a tsakanin gwamantin Tarayya da ta jihar Zamfara a kan hanyar da ya kamata a bi don kawo karshen matsalar tsaro na neman yin kafar ungulu ga yunkurin kawar da barazanar ’yan bindiga. Gwamnatin Jihar ta Zamfara dai ta sa kafa ta shure duk wani yunkuri na sasantawa da ‘yan bindiga tana mai cewa ba da ita ba, sannan ta zargi gwamnatin Tarayya da hawa teburin shawarwari da ‘yan fashin daji ba da saninta ba. Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don mu duba abin da ya sa ake samun tankiya...
Published 05/13/24
Ga alama nan ba da dadewa ba yanayin sana’ar POS a kasar nan zai sauya.  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya wajabta wa masu wannan sana’a yin rajista da Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi (CAC) zuwa nan da 7 ga watan Yulin 2024. To amma ya batun harajin da suke korafi a kai? Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don jin matsayar CAC game da biyan kudin.
Published 05/10/24
Sabuwar dokar da gwamnatin jihar Kano ta sanyawa hannu kan yin gwajin lafiya kafin aure na shan yabo da suka. A cewar gwamnatin, yawaitar yaduwar cututuka a tsakanin ma’aurata bayan aure shi ne makasudin yin wannan doka. Amma me ya sa za a daure wanda ya taka dokar tsawon shekara 5 ko tarar 500,000? Idan aka samu wanda ya taka dokar miji za a daure ko mata ko madaurin auren? Shirin Najeriya a Yau ya zanta da masu ruwa da tsaki da masana shari’a kan wannan doka.
Published 05/09/24
Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ne ya sa kowa ya koma neman kudi da mota don daukar fasinjan a Abuja. Sai dai hukumomi sun ce an dauki matakin hana duk wani mutum da bai cika ka'idojin yin tasi ba. Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilan da suka sa hukumomi ke shirin tabbatar da halascin yin kabu-kabun ga masu zaman kansu ba tare da sun yi fentin ba.
Published 05/07/24
A karshen shekarar 2023 ne dai, hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Cibiyar hana yaduwar cututtuka suka yi gargadi cewa cutar kyanda na ci gaba da zama barazana ga yara a Najeriya. Sai ga shi kwatsam an samu rahotanni game da barkewar cutar a wasu yankunan Naijeriya har ta kashe wasu mutane da dama. Shirin Najeriya a Yau ya mayar da hankali ne kan cutar ta kyanda, da yadda za ku kare yaranku daga annobar.
Published 05/06/24
Masu amfani da shafukan sada zumunta kan fada hannun masu dandantsa inda sukan yi kutse a shafin mutum har ya rasa iko da shi. Kwararru sun ce ana yi wa wasu hakan domin bata suna ko kuma neman kudi da damfara. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da kwararru a fannin samar da matakan tsaro a soshiyal midiya game da dabarun inganta tsaron shafukanku.
Published 05/03/24
Shafukan sada zumunta na ta girgiza bayan da wani labari ya bayyana game da yanayin walwalar ma’aikata da albashinsu a jihar Borno. Ma’aikata da dama sun yi ta yada hoton albashinsu na N7,000; wasu N8,000 ko N13,000 ko N15,000 ga ma’aikatan lafiya. Shirin Najeriya a Yau ya gano gaskiyar abin da ya sa gwamnatin jihar Borno ke biyan irin wannan albashi da wasu suka ce bai taka kara ya karya ba.
Published 05/02/24
Karancin man fetur na neman tsayar da al'amura cak ga al'umma a wasu sassan Najeriya. Da dama sun ce lamarin ya shafe su kaitsaye kuma sakamakon haka suna dandana kudarsu. Shin yaushe wannan lamari zai zo karshe, musamman idan yi la’akari da cewa tun a  Kamafanin Mai Na Kasa (NNPC) ya ce ya maganace matsalar? A shirin Najeriya a Yau mun tattauna da wadanda abin ya shafa sannan mu ji ta bakin masu ruwa da tsaki kan yiwuwar samun mafita nan kusa.
Published 04/30/24
Gwamnonin Arewacin Najeriya da ake fuskantar kalubalen tsaro na kokarin lalubo ko ta wace hanya a samu dabarar dakile matsalar. Tafiyar  gwamnoni 9 daga arewacin Najeriya zuwa Amurka a kwanan nan domin halartar taron tsaro ya nuna yadda suke kokarin daidaita lamarin har a matakin kasashen ketare. Saidai lamarin na zuwa ne a lokacin da wasu ke ganin an yi makamancinsa a Najeriya ba tare da halartar wani gwamna daga jihohin da suke fama da matsalar tsaron ba. Shirin Najeriya a Yau ya duba...
Published 04/29/24
Shin ka taba tunanin damammakin da za ka iya rasawa saboda rashin mallakar fasfon dan kasa a Najeriya? Yawancin mutane basu maida hankali wajen mallakar fasfo domin a tunaninsu sai idan kana kokarin ketare kasa ya zama wajibi a gare ka, amma kuma akwai damammaki da za ka iya rasawa saboda rashin mallamar shi. To ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin irin amfanin da mallakar fasfo zai iya muku da kuma damarmakin da za ku iyya rasawa.
Published 04/26/24
Ana cikin matsanancin karancin ruwa a yankuna daban-daban a Najeriya. Lamarin ya sa a 'yan shekarun mutane ke ta kokarin samar da rijiyoyin burtsatse wato 'Borehole' a turance. Sai dai a cewar masana yawanci yanzu rijiyyoyi na kafewa da kuma haifar da zaizayar kasa. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ko haƙa bohol-bohol zai iya haifar da matsala ga muhalli da kuma al'umma a anguwanni?
Published 04/25/24
Akwai abubuwan da ya kamata a rika bayyana wa mata idan za su yi aure amma kunya tana hanawa. Wasu sai sun je gidan aure suke tarar da abubuwan da ya kamata ace sun sani daga magabata, amma sai dai su tsinta a wajen kawayensu. Shirin Daga Laraba ya duba dalilan da ya sa ake kin bayyanawa mata wasu mahimman abubuwan da ya kamata su sani idan za su yi aure.
Published 04/24/24
Hukumomi sun bayyana jihohin da za a samu matsanancin zafi a Najeriya. Lamarin ya zo daidai lokacin da makarantu ke komawa hutu, inda ake fargabar yiwuwar yaduwar cututtuka a azuzuwa masu cunkuso. Shin ta wace hanya makarantu za su kauce wa yaduwar cututtuka masu alaka da matsanancin zafi? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani
Published 04/23/24
Dambarwa ta siyasa ci gaba da daukar hankali game da dakatar da shugaban jam’iyar APC na kasa Ana ta takaddama da zargin juna tsakanin jam’iyyun siyasa musamman na Kano da gwamnati mai ci a can. Toh amma wa ke wasa da hankalin wani ko rura wutar rikicin dakatar da Ganduje a jam’iyar APC, Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani a kai.
Published 04/22/24
Ba shakka dokokin kasa iri guda ne a duk inda ake a Najeriya. Sai dai ana yawan samun kotuna da yin mabambantan matsaya kan shari’a iri guda a lokuta daban-daban. Ko me ya jawo haka? Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa kotuna ke yanke hukunci daba-daban kan shari’a iri guda.
Published 04/19/24
Ana ta murnar dalar Amurka na karyewa watakila a samu saukin kayan masarufi. Sai dai a ganin wasu yadda ‘yan kasuwa suke azamar tsawwala kudi idan ta tashi ba su yi hakan ba a yayin da take saukowa. Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilin da ya zama wajibi ‘yan Kasuwa su sauke farashin kayayyaki.
Published 04/18/24
An shiga saƙe-saƙe game da mutanen da suka yi ikirarin dakatar da Ganduje daga jam’iyar APC tun daga matakin mazaba. Sai dai uwar jam’iyar ta yi watsi da hakan, inda kuma daga bisani suka zargi jami’iyar adawa. To amma ko da ace za a dauki irin wannan matakin, wa ke da hurumin dakatar da shugaban jamiyar APC na kasa a dokance? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani.
Published 04/16/24
Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ya sa komai ya sauya amma banda albashin ma’aikata. Akwai mahimman abubuwan da masu daukar albashi ba su iya yi saboda ma’aikatu da hukumomi sun kasa matsawa da albashinsu gaba. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da ya kamata mutum ya fara dubawa ta fannin albashi kafin karbar aiki.
Published 04/15/24
Wane lokaci ya fi dacewa mutum ya fara azumin sitta-shawwal? Ana yawan shiga rudani kan hakan, da kuma tunanin cewa mace wadda ake binta bashin azumin Ramadan ko ya kamata ta dauki azumin kafin biyan bashi? Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani da wasu batutuwan da ya kamata ku sani game da azumin na kwanaki shidan bayan karamar Sallah.
Published 04/12/24
Matsin rayuwa yana daga cikin abin da ya hana mutane da dama yin shagali da wannan karamar Sallah. Wasu ma basu iya yin cefanen Sallah na abincin da za a ci ballantana sabbin dinkuna. Shirin Najeriya a Yau ya zagay wasu jihohu domin yadda mutane suka yi Sallah cikin matsin rayuwa.
Published 04/11/24
Teloli iyayen haɗa gwarama! An saba kai ruwa rana a kowace Sallah idan teloli suka sha ta fi karfinsu. Sai dai ba saban ba, wani telan da muka zanta da shi ya ce ya kammala dinkunan da ya karba kakaf yayin da wani ya tsere ya bar masu kaya da wayyo! Shin wadanne dabaru ya kamata tela ya yi amfani da su wajen ganin ya sallami kowa? Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani.
Published 04/09/24