Episodes
Shirin ya duba rayuwar 'yan Nijar mazauna birnin Hamburg a tarayyar Jamus. Wasu daga cikin 'yan Nijar din sunn shafe kusan shekaru 18 zuwa 30 a kasar Jamus tare da iyalensu.
Published 01/08/20
Shirin ya dubi irin yadda kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Nijar da Senegal suka rabauta da masallatai da makarantu da wasu kasashen musulmi irin su Saudiyya da Turkiyya da Iran suka samar. Wasu na ganin hakan wata hanya ce ta cusa wasu akidu. A saurari shirin don jin karin batutuwa.
Published 12/31/19
Shirin na wannan karo ya duba batun tsarin tafiyar da ilimi a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu a Jamus da kuma irin bambancin da ke da akwai a tsakaninsu da kuma wanda ke da akwai tsakanin Jamus da Afirka.
Published 12/24/19
Bikin wankan sarauta a garin Nobi da ke cikin jihar Tahoua a Jamhuriyar Nijar ga Basaraken al'ummar Abzinawa da ke a wannan gari. Bikin da ya samu halartar manyan baki a duk fadin jihar da ma wajenta.
Published 12/17/19
Shirinmu na Taba Ka Lashe ya mayar da hankali kan tatsuniyoyi da mafi aksari ake wa kananan yara.
Published 12/10/19
Shirin ya duba A ranar bikin baje kolin littattafai na duniya da aka saba yi kowace shekara a birnin Frankfurt na nan Jamus. Babban abin da bukin ke son cimma shi ne na kara bunkasa al’adu da inganta harkokin rubutu da karatu a duniya
Published 10/29/19
Shirin ya duba batun rufe wata makarantar Islamiya da rundunar 'yan sandan jihar Kaduna a Najeriya ta yi, bisa zargin cin zarafin daruruwan kananan yara da gana musu azaba da sunan ba su tarbiyya ta gari.
Published 10/15/19
Sharuddan neman aure a masauratar Bahindi ta Bugudu a jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya
Published 10/08/19
Shirin ya duba bukin shekara-shekara na makiyaya wanda Jamhuriyar Nijar ta saba shiryawa a garin N'Gall na Jihar Agadez, bukin da aka fi sani da Sallar Lasar Gishiri.
Published 10/01/19
Matakin gwamnatin jihar Edo da ke Najeriya na inganta harkokin ilimi a makarantun gwamnati da ke fadin jihar.
Published 09/17/19
Shirin ya duba ranar harshen Hausa ta duniya da aka saba rayawa a ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara.
Published 09/03/19
Tarihin birnin Tangier na kasar Maroko da ke a nahiyar Afirka, nisan tafiyar mintuna 25 ta tekun Baharum da Spain, da kuma rawar da yake takawa a fannin huldar Turai da Afirka.
Published 08/27/19
Nazari kan asalin rikici tsakanin kabilun Fulani da na Dogon a kasar Mali da hanyoyin da za a bi wajen dinke baraka tsakanin kabilun biyu
Published 08/20/19
Taron 'yan Nijar mazauna kasar Beljiyam albarkacin zagayowar ranar samun 'yancin kan Nijar.
Published 08/13/19
Nazarin hanyoyin inganta harkar ilimi musamman na firamare da sakandare a Jihar Yobe da ke a shiyyar Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya.
Published 08/06/19
Waiwaye kan cika shekaru 50 da harba Kumbon Apollo 11 da ya kai dan Adam na farko da ya sanya kafarsa kan duniyar wata a ranar 20 ga watan Yulin 1969.
Published 07/31/19
Tabarbarewar tarbiyya a wannan zamani ya zaburar da al'umma yin hobbasa don yi wa tufkar hanci ta hanyar hada hannu wuri guda da wadanda lamarin ya shafa don daukar mataki
Published 07/23/19
A bana aka cika shekaru 100 caf da kafa makarantar fasahar gine-gine da aka fi sani da Bauhaus, wanda Walter Gropius ya kafa a shekarar 1919 a birnin Weimar na nan Jamus.
Published 07/16/19
Hukumar Raya Al'adu da Bunkasa Ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta sanya birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar cikin birnin da ya shiga kundin tarihi. Ku biyo mu cikin shirin Taba Ka Lashe.
Published 07/02/19
Tallafin da matasa marubutan litattafai su ke iya bayar wa ga al'umma a kasashen Afirka
Published 06/17/19
Duba shirye-shiryen karamar sallah musamman a garin Katsina da ke Najeriya da kuma Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar.
Published 06/04/19
A Siriya, an ceto wani bangare na kayakin tarihin masu daraja da 'yan ta'adda na kungiyar IS suka lalata, inda yanzu haka ma kwararrun masana ke aiki tukuru na gyara wadannan kayayyaki.
Published 05/28/19
Shirin ya duba tarihin rayuwar Sharif Rabi'u Usman Baba shahararren mawakin begen Manzon Allah wanda Allah ya yi wa rassuwa a wannan wata na Mayu a birnin Kano na Tarayyar Najeriya.
Published 05/21/19
Ko kun san yadda kabilar Yandam da ke jihar Adamawan Najeriya ke gudanar da bukukuwansu na al'ada? Ku biyo mu a cikin shirn na Taba Ka Lashe.
Published 05/14/19
Shirin na wannan mako ya duba yadda al'ummar Musulmi ke shirye-shiryen tarbon azumin watan Ramadana a kasashen Nijar da Najeriya da kuma falalar da ke tattare da wannan wata.
Published 05/07/19