Episodes
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne akan dambarwar siyasar Amurka inda ya rage kwanaki a kada kuri’ar zaben shugaban kasa. A cikin shirin za a ji yanayin zaben Amurka da kuma yadda zaben na bana ya zo da sabbin abubuwa da ake ganin sun sabawa demokuradiyar kasar.
Published 10/29/16
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da bikin cika shekaru 20 da jihohi 6 suka gudanar wadanda Marigayi Janar Sani Abacha ya kirkiro a shekarar 1996. Shirin ya mayar da hankali a Jihohin Gombe da Zamfara. Shin kwanliya ta biya kudin sabulu? Sannan shirin ya tabo muhawarar da ake a Majalisar Dattijai kan wani kudirin doka na Daidaiton jinsi wato kudirin doka da zai ba mata damar yin kafada da kafada da maza wanda ke yin karo da addini.
Published 10/15/16
Published 10/09/16
Shirin Dandalin Siyasa ya yi nazari kan shirin babban zaben kasar Ghana da za a gudanar a watan Disemba. Shirin kuma ya leka Najeriya game da batun fasa kwan da Hon Abdulmumin Jibril ke yi a Majalisar dokokin kasar.
Published 10/08/16
Shirin ya mayar da hankali kan sabon rikicin da ya kunno kai a majalisar wakilan Najeriya, sakamakon tsige shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Hon. Abdulmumin Jibril, wanda shi kuma ya rika fitar da wasu bayanan sirri na yadda ake almundahana yayin tsara kasafin 2016 a zauren majalisar.
Published 07/30/16
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne akan takun-sakar da ake yi tsakanin bangaren shugabannin Majalisar Dattijan Najeriya da kuma bangaren zartarwa musamman game da shari'ar da ake yi akan Sanata Bukola Saraki da Mataimakinsa.
Published 07/03/16
A cikin shirin dandalin siyasa Abdoulkarim Ibrahim yayo dubi dangane da rikicin shugabanci da ya kaure a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya. Ya kuma dubo wasu labaren daga Kano dama Bauchi Najeriya.
Published 06/19/16
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna kan karin farashin fetir da gwamnatin APC ta Muhammadu Buhari mai da'awar canji a Najeriya ta yi. Shirin ya ji ra'ayin 'Yan Najeriya  da bangaren adawa da kuma masana tattalin arziki kan yadda suka kalli matakin karin farashin bayan janye tallafin mai.
Published 05/15/16
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne kan takun sakar da aka soma tsakanin gwamnati da kungiyoyin fararen hula a Nijar kan sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Maris.
Published 05/07/16
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna kan sabanin da ake samu tsakanin bangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin Najeriya a game da Kasafin Kudi wanda har yanzu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki sanya wa hannu.
Published 05/01/16
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna kan sabanin da ake samu tsakanin bangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin Najeriya a game da Kasafin Kudi wanda har yanzu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki sanya wa hannu. Sannan shirin ya tabo rikicin Siyasa a Nijar inda ake ta cece-kuce kan yawan Ministocin da Shugaba Mahamadou Isooufou ya nada.
Published 04/16/16
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne kan dambarwar siyasar Nijar inda Shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya ce an yi yunkurin yi ma sa juyin mulki. Sannan Shirin ya tabo siyasar Najeriya.
Published 12/20/15
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da dambarwar siyasar Jihar Kogi inda ake takaddama kan wanda zai gaji Prince Abubakar Audu na APC da ya rasu kafin kammala zaben Jihar. Shirin ya kuma leka siyasar Nijar.
Published 11/29/15
Shirin Dandalin siyasa ya leka Jamhuriyyar Nijar inda Hama Amadou babban mai adawa da Mahammadou Issoufou ya dawo gida Nijar ya shafe lokaci yana buya a Faransa kan tuhumar da ake masa game da mallakar jarirai ba kan ka'idar dokar kasa ba. Shirin kuma ya yi bayani akan dambarwar siyasar Jihar Taraba a Najeriya. Shirin ya tabo batun taron PDP mai adawa da ta nemi afuwar 'Yan Najeriya.
Published 11/16/15
Shirin Dandalin Siyasa ya yi bayani game da dambarwar siyasar Jamhuriyyar Nijar inda ‘Yan adawa ke korafi akan rigistar masu kada kuri’a da tare kuma yin kira a yi garanbawul ga kotun zabe. Shirin ya tattauna da tsohon shugaban kasar Mahammane Ousmane.
Published 11/08/15
a wannan mako Bashir Ibrahim Idris ya tattauna kan rashin ja gaba da ake ganin jam'iyar PDP mai adawa a Najeriya ke fuskanta, bayan da mulki ya subuce daga nannuta ya kuma fada a hannun jam'iyar APC.  A sha sauraro lafiya
Published 09/27/15
Shirin Dandalin Siyasa ya mayar da hankali ne akan matsalar tsaro a Najeriya musamman game da hare haren kunar bakin wake da Mayakan Boko suka tsawalla a zamanin Mulkin Muhammadu Buhari wanda ya sha alwashin kawo karshen ayyukan Kungiyar.
Published 07/11/15
Shirin Dandalin Siyasa a wannan mako, Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali ne kan shugaban Hukumar Zaben Najeriya INEC Farfesa Attahiru Jega, wanda ya kawo karshen aikinsa a hukumar cikin makon da ya gabata.    
Published 07/04/15
Shirin Dandalin Siyasa na wannan mako, ya mayar da hankali ne a game da irin bashin da gwamnonin wasu jihohi ke ikirarin cewa sun gada daga wadanda suka gabace su. Bashir Ibrahim Idris ya yi dubi a game da wannan batu, kuma shi ne babban maudu'in shirin na wannan mako.  
Published 06/20/15
Rikici a Majalisun Tarayyar Najeriya, sakamakon yadda wasu 'yayan jam'iyyar APC mai mulkin kasar suka ki bin umurnin jam'iyyar na zaben wadanda ta tsayar takarar neman shugabancin Majalisun biyu. A cikin wannan shiri na Dandalin Siyasa, Bashir Ibrahim Idris ya yi mana dubi dangane da wannan badakala.
Published 06/14/15
Shirin Dandalin Siyasa ya yi nazari ne game da manyan kalubalen da ke gaban sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Published 06/07/15
Shirin dandalin Siyasa a wannan lokaci ya mayar da hankali ne akan rikici da aka tafka a zauran Majalisar kasar, rikici da ya kai ga baiwa hamata Iska tare da Bashir Ibrahim Idris.
Published 06/06/15
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da bikin Rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban Najeriya.
Published 05/31/15
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna kan rikicin Jam'iyyar PDP da ta sha kaye a zaben 2015 a Najeriya. Shirin ya mayar da hankali game da murabus din shugaban PDP Ahmed Mu'azu.
Published 05/24/15